Bayan Mutuwarsa: Karon Farko da Aka ji ta Bakin Mahaifiyar Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Falmata Abubakar, mahaifiyar shugaban Boko Haram wanda ya mutu, Abubakar Shekau, ta bayyana cewa tana matuƙar baƙin cikin cewa ɗan da ta haifa ne ya jefa miliyoyin mutane cikin baƙin ciki.

Wannan ne karo na farko da aka ji ta bakinta tun bayan mutuwar tasa.

Falmata ta bayyana wa kafar talabijin ta Trust cewa ba ta da tabbacin cewa Shekau ya haihu kafin rasuwarsa.

“Abin kawai da ke tsakanina da shi shi ne cewa ni na haife shi, amma babu wata alaƙa a tsakaninmu,” a cewarta.

“Ba zan iya tabbatar da mutuwarsa ba saboda ganina na ƙarshe da shi shekara 18 da ta gabata kenan kuma ko yana da ɗa ko a’a wannan abu ne da ban sani ba.”

Haka kuma, Falmata ta bayyana cewa Shekau ya haifar mata da baƙin ciki sosai a matsayinta na mahaifiya kuma Allah ne kawai zai yi sakayya kan duka abubuwan da ya yi.

Ta ce ko a jikinta idan yana raye ko yana mace kuma ta bar shi da Allah kan abubuwan da ya aikata.

A cewarta, Shekau ya girma kamar kowane yaro amma da ya koma Maiduguri, babban birnin jihar Borno don neman ilimin addini, sai abubuwa suka sauya.

Ta ce a nan ne ya haɗu da Muhammad Yusuf, wanda ya kafa ƙungiyar Boko Haram.

Ƙungiyar ISWAP mai adawa da Boko haram ta sanar da mutuwar Shekau a wani sakon murya da aka naɗa ranar 5 ga watan Yunin 2021.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ƙungiyar ya tayar da abin fashewa ne a jikinsa bayan da mayaƙan ISWAP suka kai masa hari a inda yake ɓoye.

Wane ne Abubakar Shekau?

Bayan da ya zama shugaban Boko Haram bayan mutuwar Muhammad Yusuf a hannun ‘ƴan sanda a 2009, Shekau ya soma sauya muradan ƙungiyar zuwa ta kashe-kashe a arewa maso gabashin Najeriya.

A ƙarƙashin shugabancin Shekau, Boko Haram ta ƙaddamar da hare-haren bam da garkuwa da mutane da ɓalla gidajen yari a faɗin yankin. Kuma daga 2014, ƙungiyar ta fara ƙwace iko da garuruwa don kafa daular Muslunci ƙarƙashin abin da ta kira dokokin Shari’ar Musulunci.

Mutane da yawa na ganin cewa shekarun Shekau ba za su haura 45 zuwa da 47 ba, kuma ya nuna goyon bayansa kan wani kamfe na masu iƙirarin jihadi a hotunan bidiyo na farfaganda inda har aka riƙa kwatanta shi da Osama Bin Laden.

“Ina jin daɗin yin kisa… kamar yadda nake jin daɗin kashe kaji da raguna,” kamar yadda ya ce a wani bidiyo.

Tun da ya karɓi shugabancin ƙungiyar, sama da mutum 300,000 ne aka kashe kuma sama da mutum miliyan biyu ne aka raba da muhallansu.

Ƙungiyar ta ja hankalin duniya bayan da suka yi garkuwa da ɗaruruwan ‘ƴan mata a shekarar 2014 daga makarantarsu a Chibok, jihar Borno wanda ya haifar da gangamin #BringBackOurGirls. Kawo yanzu ba a gano da yawa daga cikin ƴan matan ba.

Ba da jimawa ba, Amurka ta ayyana Shekau a matsayin “ɗan ta’adda na duniya” kuma ta sa tukwicin dala miliyan 7 ga duk wanda ya kamo shi.

Akidar Shekau ta yi tsananin tsauri inda har kungiyar IS ta yi fatali da ita, IS ta fice daga Boko Haram a 2016 kuma ta kafa ISWAP a madadin haka.

Tun bayan ɓallewarsu, ISWAP ta fatattaki Boko Haram daga arewa maso gabashin Najeriya kuma ta zama babbar ƙungiyar masu ta da ƙayar baya a yankin.

‘Shekau ya ɓata wa garinmu suna’
Bayan da sunan Shekau ya karaɗe duniya saboda ayyukan ta’addanci na ƙungiyarsa, ya zama abu mai wahala ga mutanen garin Shekau su yi mu’amala da sauran mutane a jihar Borno saboda mummunan sunan da ƙyama da ake nuna masu.

Yusuf Harun wanda ɗan ƙauyen Shekau ne ya shaida wa BBC cewa har yanzu kungiyar na nan.

“Abin kunya ne ka ce kai ɗan Shekau ne saboda abin da Abubakar ya yi, kuma na san mutane da yawa da suke ƙin faɗin cewa daga nan suka fito.”

Isa Sani wanda ke zaune a jihar Borno ya ce ƙyamar da ake nuna masu ta ƙaru a shekarun baya-bayan nan, saboda ya haɗu da ‘ƴan ƙauyen Shekau da ke musanta cewa su ‘ƴan garin ne ko su ce su ‘ƴan wani garin ne na daban.

“Shekau ya ɓata sunan garin har abada shi ya sa ‘ƴan garin da yawa ke ƙin faɗin su ƴan garin ne.

“Muna fata abubuwa za su sauya nan gaba idan aka samu mutanen kirki sun fito daga ƙauyen kamar likitoci da farfesoshi da za su taimaki al’umma.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here