Corona: Hukumar Lafiya ta Duniya ta Amince da Rigakafin Cutar da Indiya ta Samar

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ta amince a soma bada rigakafin annobar corona da Indiya ta samar cikin gaggawa.

Rigakafin da kamfanin Bharat BioTech ya samar na da ingancin kashi 78 ciki 100 kan annobar, wanda zai yi aiki cikin kwanaki 14 ko sama da hakan idan aka karbe shi sau biyu.

Matakin WHO zai bada damar soma shigar da allurar da aka yiwa suna Covaxin kasashe matalauta da masu matsakaicin karfi, saboda yana da saukin adanawa.

Kazalika amincewa da rigakafin zai taimakawa miliyoyin Indiyawa da tuni suka karbi rigakafin kafin ya fita kasashen ketare.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here