Manhajar Pegasus: Amurka ta Sanyawa Kamfanin Isra’ila Takunkumi

 

Amurka ta sanyawa kamfanin Isra’ila da ya kirkiri manhajar Pegasus takunkumi, da ake zargin gwamnatoci na amfani da ita wajen kutse a wayoyin ‘yan hamayyar siyasa, masu fafutika, ‘yan jarida da sauransu.

Ma’aikatar kasuwancin Amurka, ta ce ta yanke hukuncin sanyawa kamfanin takunkumi kan ayyukan da ke barazana ga tsaron kasa ko shiga harkokin kasashen ketare da ke hulda da Amurka.

Amfani da manhajar Pegasus wajen kutse ya tada jijiyoyin wuya a kasashen duniya, inda rahotanni ke cewa ana amfani da manhajar wajen muzgunawa abokan hamayya.

Kamfanin ya nuna rashin dadinsa da matakan Amurka tare da cewa zasu dauki mataki.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here