Ya Kamata a Rika yi wa Masoya Gwajin Shan Miyagun Kwayoyi Gabanin su yi Aure – NDLEA

 

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA Buba Marwa ya ce kamata ya yi a rika yi wa masoya gwajin shan miyagun kwayoyi gabanin su yi aure.

Ya yi wannan kira ne a wani taron gabatar da littafin “Legacies of a Legend” na Ambasada Bamanga Tukur.

Ya shawarci iyaye da su rika matsawa kan gwajin shan kwaya kafin su bayar da auren ‘ya’yansu.

“Ina son yin amfani da wannan damar in isar da sakon da ke raina, kuna son ‘ya’yanku mata su auri mazajen da ke shan kwaya? in kuna so to ku daga hannunku sama.”

“Kafin ko wanne, ku tabbatar kun sa yaranku sun yi gwajin HIV da na kwayoyin halitta. Ina rokonku, mu rika yin gwajin kwayoyi gabanin aure,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here