Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Fashin Daji a Kaduna

Sojojin sama na Najeriya sun kashe ‘yan fashin daji da dama a hare-hare ta sama da suka kai a wasu yankuna na Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

A cewar sanarwar, an kashe ‘yan fashin dajin da ba a san adadinsu ba a hare-hare ta sama da aka kai wa sansanoninsu da ke Ƙaramar Hukumar Chikun kusa da iyakar jihar maƙociyarta.

An kai hare-hare ta sama a wasu wurare da aka tantance a ƙauyukan Kauwuri da Gaude bayan nazarin da aka yi a kan bayanan sirri, a cewar sanarwar.

“A harin na farko jiragen saman yaki sun kai wa sansanonin ‘yan fashin dajin hari a yankin Kauwuri inda aka hango ‘yan fashin daji suna tserewa.

“Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya zo daga baya inda ya yi musu luguden wuta.

“Jiragen saman sun kuma kai hari kan wata maɓoyar ‘yan fashin daji da aka gano a yankin Gaude lokacin da suke kokarin fakewa a karkashin wasu bishiyoyi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here