Najeriya: Akalla Mutane Miliyan 120 ne Suke Fuskantar Kamuwa da Cutuka
Ma’aikatar lafiya a Najeriya ta ce sama da mutum miliyan 120 ne ke cikin hatsarin kamuwa da cutukan ƙasashe masu zafi da aka yi watsi da su a ƙasar.
Cutukan waɗanda suka haɗar da ciwon gira ko amodari da tundurmi da kuturta da tsargiya, ana kiransu da suna waɗanda aka yi watsi da su ne saboda ba sa samun kulawar hukumomi kamar sauran.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ambato wani jami’in lafiya a ƙasar na cewa cutukan rukunin wasu cutuka ne guda ashirin da suka zama ruwan dare a ƙasashe masu zafi kuma suna da alaka ta kut-da-kut da talauci da rashin tsaftar muhalli da rashin kafar samun ruwan sha mai tsafta da kuma rashin ingantaccen muhalli sai uwa-uba karancin damar samun ayyukan kula da lafiya.
Dr Kabir Ibrahim wani kwararren likita ne a Najeriya ya shaida wa BBC cewa rashin bai wa tsafta muhimmanci ita ke sake ta’azara barazanar irin wadannan cutuka. Sannan likitan ya ce cutukan sun fi addabar masu ƙaramin karfi
Read Also:
Ma’aikatar lafiyar dai ta yi ƙiyasin cewa kashi 20 cikin 100 na mutanen da cutukan za su iya shafa, ƙananan yara ne da ba su kai shekarun zuwa makaranta ba. Da kuma yaran da suka isa zuwa makaranta ne har kashi 28.
Akwai kuma manya har kashi 52 cikin 100 da suma ke fuskantar irin wannan barazana.
Dr Kabir ya ce cutar na samun wanda ba shi da kudi ko ilimin kare kansa, inda cutuka ne da suka shafai kowa da kowa da tuni an dau matakan shawo kansu.
Cutukan ana ce musu wadanda ba a damu da su ba ne saboda sun fi kama kasashe matalauta kuma ba a ba su irin kulawar da ake bai wa sauran cutuka.
Ƙwararu a fanin lafiya na cewa sai jama’a da hukumomi sun tashi tsaye don yaƙar cutukan amma gwamnati ita ce kan gaba matuƙar da gaske ana son kawar da su.
Ta ya cutukan ke yaɗuwa?
Ana daukan cutukan ta hanyar shan ruwa ko kuma iska ta yada ta kan abinci sa sauran abubuwan da ake sa wa a baki.
Sannan rashin ilimin kare kai da tsafta na taka muhimmiyar rawa wajen yada nau’ikan wadannan cutuka.
Akwai bukatar bijiro da hanyoyi masu karfi muddin an shirya kubutar da mutane daga irin wadannan cutuka masu illa.
Gargaɗi
Masana dai na cewa matsawar ana son magance irin wadannan cutuka, sai hukumomi a matakai daban-daban sun yi takun tsaye ta hanyar ware kudade na musamman a kasafin kudi da kuma wayar da kan al’umma mahimmancin tsaftar muhalli da kuma tsaftace abubuwan da ake ci.