Hukuncin da Kotun Legas ta Yanke wa Faston da ya Bada ‘Cek Din Bogi’ na $1.6m
Kotun na musamman a Jihar Legas ta yanke hukuncin daurin shekaru biyu kan wani fasto kan laifin bada cek na bogi.
Mai shari’a Taiwo ta ce wadanda suka shigar da karar sun gabatar da hujoji da ke nuna faston ya san babu kudi a asusun bankinsa amma ya bada cek din.
Kotun ta kuma umurci wanda aka yanke wa hukuncin ya biya dala miliyan 1.6 ga wanda ya yi karar cikin watanni 18.
Legas – Kotun laifuka na musamman a Ikeja a ranar Laraba ta yanke wa wani Ayodeji Oluokun, mataimakin fasto a cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), a Victoria Island Legas, hukuncin daurin shekaru biyu kan bada cheque din bogi na Dalar Amurka Miliyan 1.6 ($1.6m).
NAN ta rahoto cewa an gurfanar da Mr Oluokun ne tare da kamfaninsa, Peak Petroleum Industry Nig. Ltd., kan zargi shida masu alaka da bada cek na bogi, sata da yaudara don karbar kudi.
Mai shari’a Oluwatoyin Taiwo, a hukuncinta ta ce masu shigar da karar sun gamsar da kotu cewa an aikata laifin mika cek da sanin cewa babu kudi a asusu bankin, rahoton Premium Times.
Read Also:
Mrs Taiwo, amma, ta wanke wanda ake zargin kan tuhumar sata da karbar kudi da yaudara.
Mrs Taiwo ta ce:
“Wanda aka yi karar ya bada cek biyu na dala miliyan 1.6, wanda aka ki karba saboda babu kudi a asusun wanda ya bada.
“Bada cek tare da sanin babu kudi a asusun laifi ne.
“Idan wanda aka yi karar tabbas yana tsammanin kudi a karshen watan Yulin 2014 kamar yadda ya yi ikirari, ya kamata ya jira ya kudin ya shiga kafin ya bada cek din a ranar 24 ga wata Yulin 2014.”
Alkaliyar ta ce wanda aka yi karar ya san hakan duk da haka ya bada cek din mai dauke da kwanan watan ranar 24 ga watan Yuni.
Ta ce:
“Don haka an same shi da laifin tuhumar farko da na biyu na bada cheque na bogi.
“Amma, an wanke shi daga tuhumar sata da karbar kudi ta hanyar karya duba da cewa masu gabatar da karar sun gaza gabatar da hujjan hakan.”
Alkalin ta yanke wa wanda aka yi karar hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari da zabin biyan tara na Naira miliyan 2.
Ta bada umurnin wanda aka yanke wa hukunci ya biya dala miliyan 1.6 ga wanda ya yi karar cikin watanni 18.