Hukuncin da Kotu ta Yankewa Kishiyoyi Kan Fada Akan Mijinsu a Jahar Kaduna

 

Wata kotun Shari’a da ke zamana a Rigasa Kaduna ta bada umurnin a bawa wasu matan aure 2 masauki a gidan gyaran hali.

Daya daga cikin matan ne ta yi shigar da kara a kotu cewa an mata duka kuma an cije ta, amma daga baya alkali ya gano fada suka yi kuma sun cije juna.

Alkalin ya bada umurnin a tsare su na sati biyu a gidan gyaran hali don su koyi darasi kafin yanke hukunci, yayin da mijinsu ya ce akwai yiwuwar ya ake su.

Jihar Kaduna – Wata kotun shari’a da ke zamanta a Rigasa, Jihar Kaduna ta tsare maan wani Danlami Tasiu a gidan gyaran hali tsawon sati biyu saboda fada ta cizon junansu a unguwar Bukuru.

Alkalin kotun, Salisu Abubakar-Tureta ya bada umurnin ne bayan ya gano matan biyu sun cije junansu a maimakon ikirarin da daya ta yi na cewa bata da laifi kuma ana musguna mata, rahoton Daily Nigerian.

Mr Abubakar-Tureta ya ce an tsare su ne domin su samu damar yin tunani da nazari kan abin da suka aikata, ya kuma dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Fabrairu.

Yadda abin ya faru

Daya daga cikin matan, Azima Usman Tasiu ce ta yi karar abokiyar zamanta a kotun kan zargin dukanta da cizonta.

Azima ta shaida wa kotun cewa ita ce matar Tasiu ta uku, ta kara da cewa an mata duka ne saboda karamin rashin jituwa da ya shiga tsakaninta da dan Aisha.

A cewar Azima, ranar girkinta ne ta tafi zuwa dibo ruwa daga rijiya, inda ta hadu da dan wanda aka yi karar.Ta umurci ya bari da diba ruwa amma ya ki.

Ta ce:

“Mahaifiyarsa ta zo ta tsinke gugar dibar ruwar ta tafi da shi dakinta.

“Na bi ta domin in karbo; ina shiga dakinta, ta mare ni, ta fara duka na har da cizo.”

Aisha, wacce ita ce matar Tasiu ta biyu, ta ce Azima ce ta fara kama ta da dambe bayan ta doki dan ta sannan ta duke ta ta kuma cije ta a kafada.

Alkali ya zurfafa bincike

Alkalin, wanda ya yi mamakin ikirarin da suka yi, ya bukaci su nuna masa bangaren jikinsu inda aka yi cizon kuma suka nuna masa.

Alkalin ya ce abin da ya faru fada suka yi ba wai mutum daya aka zalunta ba.

Shima, Tasiu, ya shaida wa kotun cewa ya tarar da su suna fada ya yi kokarin raba su amma bai yi nasara ba.

Mr Tasiu ya ce ko wane hukunci kotu ta yanke a ranar 28 ga watan Fabrairu, akwai yiwuwar zai saki dukkansu su biyun.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here