Kano: Kotun Majistire ta zartar da Hukuncin Bulala Kan Wasu Matasa

 

kotun majistire karkashin jagorancin mai shari’a mallam Farouk Ibrahim ta zartar hukuncin bulala 12 kan wasu matasa.

Alkalin ya zartar da hukuncin kan Muhammad Sani da Saddam Ali bayan ya same su da laifin siyar da miyagun kwayoyi.

Mai kara Mallam Muhammad Bichi ya ce laifin ya sabawa sashe na 403 na kudin Panel Code.

Wata kotun Majistare a ranar Talata ta yankewa mutum biyu, Muhammad Sani, dan shekara 24, da Saddam Ali, mai shekaru 27, hukuncin bulala 12 saboda kama su da laifin siyar da tabar wiwi da wasu miyagun kwayoyi.

Masu laifin, wanda ba a bayyane adireshin su ba, an kama su da laifin mallakar tabar wiwi da kuma wasu kayan maye, Daily Nigerian ta ruwaito.

Alkalin kotun, Mallam Farouk Ibrahim, ya tabbatar da laifin su bayan sun karyata zargin mallakar miyagun kwayoyin.

Ibrahim ya umarci ayi musu bulala 12 kowanne bayan sun roki ayi musu sassauci.

Tun da farko, mai kara Mallam Muhammad Bichi, ya fadawa kotu cewa masu laifin sun aikata laifin ranar 21 ga Disamba da misalin 9:00 na dare a Plaza, karamar hukumar Fagge da ke Jihar Kano.

Bichi ya ce jami’an yan sandan Fagge ne suka kama masu laifin da sacet goma na Rophypnol, wata mummunar kwaya, da dauri daya na tabar wiwi da wani abu mai ruwa ruwa da ake zargin mai bugarwa ne.

Ya ce laifin ya sabawa sashe na 403 na kundin Penal Code.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here