Yadda Kudaden Intanet ke Zama Barazana ga Kasashe – Abdulrasheed Bawa
Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya bayyana yadda kudaden intanet ke zama barazana ga kasashe.
Ya bayyana cewa, ana amfani da Bircoin da Ethereum wajen biyan kudin fansar hare-haren yanar gizo.
Ya kuma jaddada cewa, lamarin ya shafi kasashe da dama, kuma yana kara ta’azzara har a kasashen da suka ci gaba.
England – Abdulrasheed Bawa, shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ya ce kudaden intanet sun zama kyakkyawan zabi ga mutanen da ke gudanar da hada-hadar kudi ba bisa ka’ida ba, TheCable ta rawaito.
Bawa ya fadi hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a ranar Litinin 6 ga watan Satumba, a taron kasa da kasa na Cambridge karo na 38 kan laifukan tattalin arziki, mai taken, ‘Laifin Tattalin Arziki: Wa Ya Biya kuma Wa Ya Kamata Ya Biya Farashi?’
Cibiyar Adana Bayanai ta Duniya kan Tsararrun Laifukan Tattalin Arziki (CIDOEC) a Kwalejin Jesus ta Jami’ar Cambridge a Burtaniya ce ta shirya taron.
A cikin wata sanarwa da Wilson Uwujaren, kakakin EFCC ya fitar, ya ambato Bawa na cewa amfani da kudaden intanet da ‘yan ta’adda ke yi yana zama barazana ga tattalin arzikin duniya.
A cewarsa:
Read Also:
“Laifukan tattalin arziki, wadanda galibi haramtattun ayyuka ne da ake aikatawa don cin ribar kai, suna shafar mahimman tsarin tattalin arzikin duniya, suna haifar da babbar illa ga tsarin kudi na duniya da hana kasashe masu tasowa albarkatun da ake bukata don ci gaba mai dorewa.”
“‘Yan ta’adda a yanzu suna zabar yin hulda ko karbar haramtattun kudaden (kamar kudin fansa) na kai hare-hare ta yanar gizo ta hanyar kudaden intanet tare da Bitcoin da Ethereum a matsayin mafi yawan wadanda ake amfani dasu a wadannan musaya.”
Ya kuma ce kasashen da suka ci gaba su ma basu tsira daga irin wadannan matsaloli da suka saba wa doka ba, idan aka yi la’akari da “yaduwar laifuka ta yanar gizo wadanda ke zama barazana ga zaman lafiyar cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya”.
Ya kara da cewa
“Yayin da wadanda ake cuta ke ci gaba da shan wahala a duniya sakamakon illolin ta’addancin kudi, kai tsaye ko a kaikaice a matsayin wani bangare na tsarin zamantakewa, kudurin wanda ya biya ko wanda ya kamata ya biya farashi ya zama mahimmin ma’aunin tsarin shari’ar laifi a wurin.
Ya kara da cewa shari’a ba tare da nuna bambanci ba zai zama mai mahimmanci wajen tabbatar da cewa “masu aikata ayyuka ba wadanda abin ya shafa suke biyan farashin laifukansu”.