Dokar Hana Makiyaya Kiyo a Kudancin ƙasar Nan: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa ga Jahar Delta

 

 

Wata ƙungiya da ba’a santa ba tayi watsi da dokar hana makiyaya kiyo a fili a kudancin ƙasar nan

Ƙungiyar ta bayyana matakin da zata ɗauka matuƙar gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, ya cigaba da goyon bayan wannan dojar.

A wani taro da gwamnonin kudu sukayi, sun amince da kafa dokar hana kiwo a fili a yankunan su.

An shiga yanayin tsoro da tashin hankali a jahar Delta bisa barazanar da wata ƙungiya tayi cewa zata kai hari babban birnin jahar kan nuna goyon bayan dokar hana kiwo da gwamnan jahar, Ifeanyi Okowa, yayi.

Jaridar punch ta ruwaito cewa, ƙungiyar tayi barazanar ne a wata takarda da babu sanya hannun kowa a ciki, wacce aka yi wa take da “Gargaɗin yan jahadin Fulani:

buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga jahar Delta,” kuma takardar na ɗauke da kwanan watan 13 ga Yuni.

Takardar wacce aka liƙa ta a wasu sassan jahar ranar Lahadi 13 ga watan Yuni, ta yi garhaɗin cewa za’a kawo hari Asaba da Agbor, jahar Delta, matuƙaɗ gwamna ya gaza cika musu buƙatunsu nan da wanni 72.

Ƙungiyar tace:

“Muna buƙatar gwamnan Delta ga gaggauta canza matsayar da ya ɗauka kan hana makiyaya kiwo a fili a jahohi 17 cikin awanni 72 daga ranar da aka rubuta wannan wasikar.”

“Sannan kuma a jiye matsayinsa na mai magana da yawun gwamnonin da suka amince da wannan dokar nan take.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here