Muna so a Biya mu Kudin Diyya – Iyalan Wanda Dogarin Gbajabiamila ya Harbe

 

A wasikar da lauyansu ya aikewa Kaakin majalisa, sun bukaci a biya diyya.

Tuni dai Gbajabiamila yayi alkawarin kula da iyalan mamacin kuma yaransa sun zama nasa.

Iyalan mamacin sun dauki Mike Ozekhome matsayin lauyansu.

Iyalan Ifeanyi Okereke, mai sayar da jaridar da dogarin Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya kashe makon da ya gabata sun bukaci a biyasu diyyan milyan dari biya (N500m).

A wasikar da Lauyansu, Mike Ozekhome, ya aikewa Gbajabiamila, sun baiwa Kakakin kwanaki bakwai su biya kudin ko a kaishi kotu.

A wasika mai ranan wata 23 ga Nuwamba, Mr Ozekhome, ya ce mahaifin mamacin, Okorie Okereke, da kaninsa, Destiny Okereke, suka umurceshi ya bukaci kudin.

“Wadanda suka daukeni aiki sun bukaci wadannan abubuwa: Kayi amfani da ofis dinka mai alfarma wajen tabbatar da an hukunta hadiminka (Abdullahi Hassan) wanda ya kashe mutum bai gaira, ba dalili.”

“Ka biya diyya ga iyalan Okereke da kudi N500,.” “Kudin ba zai dawo da rayuwar ‘dansu, miji, da mai taimakonsu ba.Amma akalla zai taimaka musu wajen huce zafi.”

“Ka sani cewa an bani umurnin idan baka biya wadannan bukatu ba ko kayi watsi da bukatun cikin kwanaki bakwai da rubuta wasikar nan, zamu shigar da kara kotu,” wasikar yace.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here