Philip Shekwo: Gwamnan Nassarawa Yayi Kudirin Kama Makasan Shugaban APC
Gwamnan jihar Nasarawa ya sha a alwashin zakulo yan bindigan da suka kashe shugaban APC na jihar.
A daren ranar Asabar ne makasan suka kai farmaki gidansa sannan suka tsere da shi.
An kuma tsinci gawarsa a safiyar ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya bayyana cewa za a bankado makasan Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar, Philip Shekwo.
Yan bindiga ne suka sace Shekwo daga gidansa da ke Lafia, babbar birnin jihar a daren ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba.
An tattaro cewa sun yi musayar wuta da jami’an tsaro da ke aiki da Shugaban na APC kafin suka tsere da shi.
Raman Nansel, kakakin yan sandan jihar Nasarawa, ya bayyana cewa an kashe Shekwo yayinda aka gano gawarsa a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba, jaridar TheCable ta ruwaito.
Read Also:
A wata sanarwa da ya saki da yawun Sule, babban sakataren labaran gwamnan, Ibrahim Addra, ya ce makasan Shugaban na APC ba za su ci bulus ba.
Ya ce za a yi farautar makasan sannan a hukunta su daidai da yadda doka ta tanadar.
“Mun sami labarin kisan Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na jihar Nasarawa, Philip Tatari Shekwo, cike da alhini da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi, bayan sun shiga gidansa ta karfin tuwo a daren jiya,” in ji sanarwar.
“Addu’ata da tunanina na tare da iyalan marigayi Shekwo. Ya kasance miji nagari, jigo, salihin mutum mai kuma biyayya ga jam’iyya.
“Ina son bayan da tabbacin cewa makasan sa ba za su ci bulus ba. Tuni jami’an tsaronmu suka fara gudanar da bincike a kan lamarin domin gano masu laifin da kuma hukuntasu.”
Jaridar Thisday ma ta ruwaito cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Sule sun sha alwashin tsamo makasan Shugaban na APC a jihar Nasarawa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emmanuel Bola Longe, wanda ya tabbatar da hakan a wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da jaridar Leadership, ya ce ‘yan bindiga masu tarin yawa ne suka tsinkayi gidan shugaban APC.