Kudu: Abinda Muke So Shugaba Buhari ya yi Mana

 

An gudanar da taro tsakanin gwamnoni da sauran masu fada aji a yankin kudu maso kudu da tawagar gwamnatin tarayya.

A yayin taron, jiga-jigan yankin kudancin kasar sun gabatarwa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu muhimman bukatu biyar.

Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa ne ya jagoranci tawagar ta gwamnatin tarayya zuwa taron wanda aka yi a Port Harcourt.

Gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin kudu maso kudu sun gana da wata tawaga daga gwamnatin tarayya a ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, a Port Harcourt, jihar Rivers.

Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Farfesa Agboola Ibrahim Gambari, ne ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayyar zuwa wajen ganawar.

An gudanar da taron ne domin magance sakamakon zanga-zangar EndSARS da sauran manyan lamura da suka addabi yankin.

Shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso kudu kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya gabatar da wasu muhimman bukata a gaban tawagar a madadin yankin.

Legit.ng ta lissafo jerin bukatun da yankin ta gabatar.

1. Sauya fasalin lamura, tsarin gwamnati na gaskiya da mika iko ga gwamnatocin kasa.

2. Mayar da hedkwatar dukkanin manyan kamfanonin mai zuwa kudu maso kudu.

3. Samar da rundunar yan sanda ta jiha.

4. Kammala hanyoyin gabas maso yamma da dukkanin sauran hanyoyin tarayya a yankin.

5. Farfado da manyan tashoshin ruwa na yankin a Port Harcourt, Calabar da Warri.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here