In Kun Isa ku ba wa Kudu Tikitin Shugaban Kasa 2023 – Umahi Zuwa PDP
Gwamna Umahi ya sake aika wani muhimmin sako zuwa ga tsohuwar jam’iyyarsa, PDP, gabannin 2023.
Gwamnan na jihar Ebonyi ya ce yana zuba ido don ganin jam’iyyar adawar ta kunyata shi ta hanyar mika tikitinta na shugaban kasa a 2023 ga yankin kudu maso gabas.
Gwamnan ya kuma bukaci jam’iyyar da ta janye daga kai masa hari.
Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya ce yana jira don ganin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bashi kunya ta hanyar mika tikitinta na shugaban kasa a 2023 zuwa yankin kudu maso gabas.
Read Also:
Jaridar Sun ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da Sanata Orji Uzor Kalu, tsohon gwamnan Abia, ya shirya masa wani taron cin abincin dare a Abuja a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba.
Ku tuna cewa Umahi ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, inda ya bayyana rashin adalci da PDP ke yi wa kudu maso gabas a matsayin dalili.
Ya yarda cewa ya kamata PDP ta sakawa yankin kudu maso gabas kan biyayyar da take mata ta hanyar mika mata tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023.
Umahi ya kuma fada ma PDP cewa ta daina kai masa hari, cewa babu wani amfani kan hakan.
Gwamnan na jihar Ebonyi ya ce bai caccaki jam’iyyar mai adawa ba tunda ya koma APC illa kawai ya bayyana rashin adalcin da take yi wa yankin kudu maso gabas.
Sai dai, ya kara da cewa tsohuwar jam’iyyar nasa tana da hakkin yin fushi, inda yace ba zai hada kowani lamura da shugabannin adawa ba.