Ƙudurin Cire Kariya ga Gwamnoni ya Tsallake Karatu na Biyu a Majalisar Wakilai
Ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu ya tsallake karatu na biyu, a majalisar wakilan Najeriya.
Ƙudurin na daga cikin gwamman ƙudurorin da majalisar ke aiki a kansu, a wani ɓangare na yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999.
Read Also:
Cikin abubuwan da ƙudirin ke fatan cimmawa idan ya zama doka zai kuma tabbatar da rigar kariya ga shugaban ƙasa.
Ƙudurin na fatan cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa, gwamnoni da mataimakansu zai taimaka wajen magance matsalar cin hanci da rashawa, hana ɗaukar hukunci a kansu sakamakon wani laifi da suke aikatawa da ƙarfafa tsare gaskiya a tsakanin masu riƙe da muƙamin gwamnati.
Sai dai ƙudurorin dokar na buƙatar amincewar duka majalisun dokoki biyu, na wakilan da na dattawan kafin ya kai ga shugaban ƙasa, wanda zai rattaba hannu a kansa sannan ya zama doka.