Kudurin Kungiyar PYB FRONTIERS Kan Gwamnan Jahar Kogi

Kungiyar PYB FRONTIERS ta fara bugawa Yahaya Bello gangar takarar a 2023.

Tace Gwamnan ya fi dacewa ya zama Shugaban kasa bayan Muhammadu Buhari.

Daga dalilan magoya bayan Yahaya Bello shi ne ya kawo hadin kan kabilu a Kogi.

Wata kungiya ta magoya bayan Yahaya Bello ta fito ta na jaddada kiranta na cewa gwamnan ya dace ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023.

Wannan kungiya mai suna PYB FRONTIERS ta yi kira ga mutane su marawa gwamnan na jahar Kogi baya domin ganin ya gaji Muhammadu Buhari.

Jaridar Vanguard ta rahoto shugaban kungiyar ta PYB FRONTIERS, Hans Mohammed ya na cewa sun fara kokarin ganin APC ta tsaida Yahaya Bello.

Hans Mohammed yake cewa gwamnan ya yi kokari a bangaren ilmin boko, kiwon lafiya, sha’anin tsaro da kuma yaki da annobar COVID-19 a jahar Kogi.

A dalilin wannan ne kungiyar magoya bayan ta ke ganin Alhaji Yahaya Bello ya cancanci jam’iyyar APC ta ba shi tikitin takarar shugaban kasa.

A cewar Mohammed, gwamna Bello ya lashe kyaututtuka a gida da ketare a dalilin kokarin da yake yi na kare lafiya da dukiyar mutanen jahar Kogi.

Jaridar ta rahoto Mohammed yana cewa abin da ya dace shi ne gwamnan ya samu babbar kujera.

Kungiyar tace an ba gwamnan lambar yabo a bangaren ritita dukiyar al’umma, sannan ya taka rawar gani a harkar noma inda ya gina kamfanin casar shinkafa a Yagba.

Bayan haka, kungiyar ta ce gwamnatin Bello ta kawo zaman lafiya tsakanin kabilun da ake da su a jahar Kogi, ta hanyar ba kowane bangare mukamai.

Duk a game da zaben na 2023, kun ji cewa jigon APC, Rochas Okorocha ya na kiran ‘Ya ‘yan PDP da jam’iyyar APC duk su dunkule domin a gyara Najeriya.

Sanata Rochas Okorocha ya bayyana haka ne bayan gwamnan Ribas ya gayyaci jagoran APC domin ya kaddamar da wasu ayyuka da aka yi.

Okorocha ya ce Najeriya na bukatar ‘Yan siyasan kirki su hada-kai da nufin kawo gyara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here