‘Yan Bindiga Sun Halaka ‘Dan Takarar Kansila na Jam’iyyar PDP

 

Yan bindiga sun halaka dan takarar kansila a jahar Delta.

‘Yan bindigan sun kuma sace wasu mutane biyu da ke tare da shi.

Rundunar ‘yan sandan Jahar Delta ta tabbatar da afkuwar lamarin.

‘Yan bindiga sun kashe dan takarar kansila na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben da za a gudanar a ranar 6 ga watan Maris a Delta, Mista Elliot Ofa.

The Nation ta ruwaito cewa yan bindigan sun sace wasu mutane biyu tare da shi.

Sai dai a tabbatar ko kashe shi na da alaka da siyasa ba sakamakon wasu na zargin cewa tun farko wasu basu so aka nada shi a jam’iyyar ta PDP.

An gano, cewa lamarin ya faru ne a layin Jesse/Oben kusa da iyakar jahohin Delta da Edo.

Rahotanni sun ce an sace marigayin da wasu mutane biyu a yayin da suke dawowa daga ofishin hukumar zabe mai zaman kanta na jahar, DSIEC, a Asaba yayin da yan bindigan suka tare motarsu suka harbe shi ya kuma mutu.

Kafin rasuwarsa, marigayin shine tsohon kansilar muhalli na karamar hukumar Ethiope-West.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jahar, DSP, Onome Onovwakpoyeya ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Ta ce: “Sun ce a Jahar Edo abin ya faru, ba a Delta ba.” A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jahar kasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here