Bishop Kukah ya Sake Sukar Mulkin Shugaba Buhari

Bishop Mathew Kukah ya sake caccakar mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Malamin ya nanata cewa ba zai yi shuru akan abubuwan da kefaruwa a kasar ba.

Yace duk sadda matsala ta kunno kai dole ne ya fito yayi magana saboda yana da ‘yanci.

Revd. Matthew Kukah, bishop na Katolika na Sakkwato, ya sake caccakar gwamnatin Najeriya.

Kukah a cikin hudubarsa ta baya-bayan nan ya koka kan yadda Najeriya ta zama kazamar kasa, cike da tarkace, yaudara, karya, cin amana, da kuma rikita-rikita inda duhu ya mamaye komai.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 6 ga watan Janairu, yayin da yake gabatar da hudubarsa a babban cocin Katolika na St Joseph, Kaduna, a lokacin da ake gudanar da hidimar Archbishop Peter Yariyock Jatau, Archbishop na Kaduna Catholic Diocese.

Shugaban addinin wanda ya kare kansa a sakonsa na Kirsimeti na 2020 wanda ya haifar da martani, ya dage cewa a matsayinsa na malami ba zai iya yin shiru game da abubuwan da ba daidai ba, ya kara da cewa hakkinsa ne ya kula da birnin.

A cewar Kukah, ya kamata ya daga muryarsa a matsayin mai tsaro a duk lokacin da ya hango hatsari a kasar.

Idan za a iya tunawa Kukah ya yi bayani lokacin bikin Kirsimeti wanda ya jawo suka daga magoya bayan Shugaba Buhari.

Malamin siffanta Buhari da nuna kabilanci, ya kara da cewa da a ce dan kudu ne ke mulki a yau, da an yi masa juyin mulki.

Sakon ya girgiza magoya baya da masoya shugaban wadanda suka yi amfani da shafukan sada zumunta inda suka zargi Kukah da ruruta wutar fitina da dumama siyasa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here