Suna Son ƙulla Haɗaka da ba za ta yi Tasiri ba da Nufin Kawar da APC – Ganduje
Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya ce duk wata haɗaka da jam’iyyun hamayyar ƙasar ke shirin yi da nufin kawar da APC a zaɓen 2027 ba za ta yi tasiri ba.
Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga manema labarai a jihar Kaduna lokacin ziyarar – da ya jagoranci shugabannin jam’iyyar wajen kai wa tsohon shugaban ƙasar – Muhammadu Buhari.
Read Also:
Gabanin ziyarar su Gandujen, tawagar jagoran adawar ƙasar, Atiku Abubakar tare da tsoffin gwamnonin jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da Sanata Ahmed Makarfi da kuma Sanata Aminu Waziri Tambuwal ta fara kai wa Buhari ziyara a gidan nasa.
Ganduje ya ce ziyarar su Atikun ba ta ɗaga musu hankali ba, saboda a cewarsa ”suna son ƙulla wata haɗaka da ba za ta yi tasiri ba”.
”Daga abin da muka gani mutane ne da ba za su iya haɗuwa ƙarƙashin inuwa guda ba”, in ji shi.
Shugaban jam’iyyar ta APC ya ce a shirye suke kuma sun san yadda za su ɓullo wa lamarin kodayake ya ce ba zai faɗi dabarar da za su bi ba.
Ganduke ya ce duk da cewa a yanzu haka APC na da iko da jihohin ƙasar 21, har yanzu jam’iyyarsu na hangen ƙarin wasu jihohin.
”Ko dai wasu gwamnonin da kansu su dawo jam’iyyarmu, ko kuma jihohin su dawo hannunmu ta hanyar zaɓe.”