Kungiyar ci Gaban Harkokin Addinin Musulunci ta Nada Sabon Mataimakin Shugaba

Kungiyar ci gaban harkokin addinin musulunci ta sanar nada Alhaji Rasaki Oladejo a matsayin sabon mataimakin shugaba.

Oladejo wanda kwarrarre ne a fannoni da dama ya maye gurbin marigayi Alhaji S. O. Babalola wanda ya rike mukamin har zuwa 2 ga Oktoba 2019 lokacin rasuwar sa.

Oladejo ya rike mukamai da dama daga ciki akwai shugabancin Nawair-Ud-Deen daga 2013 zuwa 2019.

Majalisar Kolin harkokin addinin musulunci (NSCIA) karkashin jagorancin shugaban ta sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta nada Alhaji Rasaki Oldejo, a matsayin mataimakin shugaba (daga yankin kudu) na kungiyar.

Mataimakin sakatare, NSCIA, Prof. Salisu Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook na Majalisar a ranar Alhamis 24 ga watan Disambar 2020.

Ya ce Alhaji Oladejo ya maye gurbin marigayi Alhaji S. O. Babalola, wanda shi ne a mukamin kafin rasuwar a ranar 2 ga Oktoba, 2019.

A cewar sa, Oladejo, wanda ba’a dade da nada shi matsayin shugaban al’ummar musulmin Najeriya yankin kudu maso yamma (MUSWEN), babban jagoran addini ne, masanin tattalin arziki, malamin addinin musulunci, kuma mamba ne a kwarrarrun makarantu.

“Shi ne shugaban kwamitin tattalin arziki, kudade da tsare tsaren ci gaba daga watan Mayu 2013 zuwa Nuwamba 2014.

Kuma shine shugaban kungiyar Nawair-Ud-Deen na kasa (wata kungiyar addinin musulunci da aka kafa a 1939) daga 2013 zuwa 2019. Shine shugaban, Mountain Investment and securities Limited, mamba daga hukumar chanjin kudade,” a cewar Shehu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here