Tallafin da Kungiyar CACOVID Zata Bayar

Gamayyar kungiyoyi masu yaki da annobar korona, CACOVID ta ce zata tallafawa matasa da ‘yan kasuwa a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan banar da ‘yan daba suka yi a wasu jihohin Najeriya yayin zanga zangar EndSARS.

Ayyukan da CACOVID zata yi sun hada da samar da cibiyoyin lafiya, bada kayayyakin abinci, da sauransu don tallafawa gwamnati.

Gamayyar kungiyoyi masu masu yaƙi da COVID-19 (CACOVID) a Najeriya, sun sanar da bayanan cigaban ayyukansu da kuma niyyarsu ta tallafawa gwamnati a ƙoƙarin sake gini don farfaɗo da tattalin arziƙin kasar.

Hakan ya biyo bayan tashin hankalin da ƴan daba waɗanda suka gwace ragamar zanga-zangar EndSARS suka haddasa kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Zanga-zangar wadda ta jawo asarar rayuka ,dukiyoyi da tsayawar al’amura cak a jihohin da abin ya shafa.

Lokaci da ake fayyace kuɗaɗen da CACOVID ta kashe, Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin ƙasa, ya bayyana cewa ƙungiyar ta bada gudunmawar kuɗaɗe maƙudai.

“Ƙungiyar ta karɓi naira biliyan 39.64 a matsayin gudunmawa daga mambobinta, sannan ta kashe naira biliyan 43.272 a tsare tsare da ayyuka daban daban.

Ayyukan sun haɗar da, gina cibiyoyin lafiyar ware masu cuta na naira biliyan 4.194, da kashe naira biliyan 9.017 wajen siyo kayan aikin lafiya da magunguna.

Sai naira biliyan 28.7 da aka kashe a kayayyakin abincin tallafi, gami da wayar da kan al-umma a jihohin Najeriya ta hanyar kafafen yaɗa labarai.

Emefiele ya bayyana cewa CACOVID ta ɗauki matakan ne a matsayin tallafawa gwamnati don sauƙaƙawa gwamnati farfaɗo da tattalin arziƙinta wanda annobar ta girgirza da kuma fargarbar da aka shiga kwanan nan.

Da yake magana akai Gwamnan Babban Bankin, ya ce; “Wannan yunƙuri na daga cikin muhimman matakai ne na gina gaskiya tare da daƙile tashin hankali anan gaba cikin al’ummarmu.

“Zai kuma dace da ƙoƙarin da gwamnati keyi don samarwa matasa aikinyi da kuma ƙa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here