Kungiyar Yarabawa ta Koka da Rashin Tsaro

Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta koka kan tarbarbarewar tsaro a sasan Najeriya.

Kungiyar ta yi wannan jawabin ne yayin martani kan kisar basarake Olufon na Ifon, Isreal Adeusi da ‘yan bindiga suka kashe.

Kungiyar ta ce lokaci ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari zai dage damtse don tabbatar da tsaro a kasar.

Wata ƙungiyar ƙabilar Yarabawa a ranar Juma’a ta nuna damuwarta akan kashe Olufon na Ifon a jihar Ondo, Oba Israel Adeusi wanda wasu ƴan bindiga da har yanzu ba’a gano su ba suka aikata.

Sun bayyana kisan nashi a matsayin kashe da yawa, inda sukayi kiran ga rundunar ƴan sanda kan ta zaƙulo makasan kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

Afenire ,tace kisan Olufon ya zo musu lokacin da basa gama farfaɗowa daga kisan ƴar shugaban ƙungiyar ba, Mrs Funke Olakunrin.

Wadda ake tuhumar wasu makiyaya da aikata kisan, baya ga sauran kashe kashe da har yanzu ƴansanda suka gaza warwaresu.

Lokaci ya yi da shugaban ƙasa Muhammad Buhari zai miƙe tsaye ya tsare Najeriya ya kawo tsarin tarayya da zai inganta tsaron cikin gida.

Afenire ta bayyana hakan a wani bayani da ta fitar mai taken” kisan Olufon da rashin tsaro” ta hannun Sakatarenta na ƙasa Mr Yinka Odumakin.

Sun ƙara bayyana cewa Afenire ta zo wuya da yawan kashe ƴan ƙasa da ake yi a faɗin ƙasar. Afenire ta jajantawa iyalan Olufan,da mutanen garin Ifon,Jihar Ondo,da al-ummar Yoruba bakiɗaya.

Ƙungiyar tayi tir da Allah-wadai da afkuwar lamarin.

Afenire lokacin da take kiran ƴansanda kan lamarin ta bayyana kisan nasa a matsayin gazawa da rashin iya aikin jam’an tsaron Najeriya wajen kare rayuka da dukiyar al’umma.

“Kisan gillar yazo muna tsakiyar jimamin kashe ƴar shugaban Afenifere, Mrs Funke Olakunrin, wadda ake tuhumar wasu makiyaya”.

“Akwai kashe kashe da ake a ƙasashen yarabawa wanda ƴan sanda suka gaza daƙile su.”

“Abin har ya kai jallin ana kashe manyan mutane masu daraja ga muhimmanci ga al’umma da cigabanta wanda ke nuna rashin tsaro a ƙasa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here