Janye Tallafin Fetur: Kungiyar ƙwadago za ta Shiga Yajin Aikin Gargaɗi

 

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta sanar da aniyar shiga yajin aikin gargaɗi na kwana biyu a kan matsin rayuwa da ‘yan ƙasar ke ciki sakamakon janye tallafin fetur.

NLC ta ce za ta gudanar da yajin aikin ne a ranakun Talata da Laraba mai zuwa.

A ranar da aka rantsar da shi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye tallafin man fetur, yanayin da ya haifar da tsadar litar man fetur a gidajen mai daga naira 197 zuwa 617.

NLC ta nuna ƙin amincewa da matakin gwamnati da aiwatar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.

Shugaba Tinubu ya sha ganawa da ‘yan ƙwadagon a kokarin ganin an cimma daidaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com