ASUU: Kungiyar Kwadago za ta Gudanar da Zanga-Zangar Kwana Biyu a Najeriya

Kungiyar Kwadago a Najeriya na shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga ta kwana biyu a fadin kasar saboda nuna goyon bayanta ga kungiyar malaman jami’o’in kasar ta ASUU

A wata sanarwa da kungiyar ta aike wa shugabannin rassanta na jihohi, mai dauke da sannanu shugaban kungiyar na kasa Kwarade Ayuba Wabba da sakataren kungiyar Emmanuel Ugboaja.

Kungiyar ta yi kira ga rassan nata na jihohi da su shirya gudanar da gagarumar zanga-zangar ranakun 26, da 27 ga watan Yulin da muke ciki, saboda jan hankalin gwamnatin tarayya, ta kammala tattaunawa da kungiyar malaman jami’o’in, domin bude jami’o’in kasar.

A jiya ne dai tsohun shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa Chif Wole Olanipekun (SAN), ya ce ya kamata a dauki batun yajin aikin malaman jami’o’in kasar a matsayin wani babban al’amari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here