Amurka na Jefa Kuri’a Kan Batun Zubar da Ciki
Masu jefa kuri’a sun yi gagarumar nasara inda suka bayyana cewe ba sa son yin garanbawul ga ƙundun tsarin mulkin jihar wanda yace babu ‘yancin zubar da ciki.
Wannan shi ne gwajin farko na kuri’a akan lamarin tun lokacin da kotun kolin Amurka ta amince da jihohi akan su haramta zubar da ciki.
Da kuri’ar da aka jefa ya haramta zubar da ciki, ‘yan majalisu za su iya hana zubarwa a jihar.
Tambayar da aka saka akan takardar kuri’ar ta jawo muhawarori masu zafi tun bayan da kotun kolin Amurka watanni biyu da suka wuce, da ya soke dokar Roe v Wade ta 1973 wanda ya hallasta zubar da ciki a duk fadin kasar.
Read Also:
A lokacin da aka soke Roe v Wade, shugaba Biden ya ce ‘yancin zubar da ciki zai kasance batu mai muhimmanci ga masu jefa kuri’a. Abun da ya faru a Kansas ya kasance shaidar abun da ake tunani.
Donald Trump yayi nasara a Kansas da maki 15 shekaru 2 da suka wuce, amma yanzu ya jefa kuri’ar amincewa a kare ‘yancin zub da ciki, lamarin da ake gani a matsayin babbar nasara.
A yanzu wata kariya ce, sannan za a tabbatar da sakamakon a hukumance a cikin mako daa.
Amma ga ‘yan Democrats da masu kungiyoyin da ke goyon bayan zub da ciki, wannan alama ce da ke nuna cewa Amurkawa na matukar bakin ciki da soke ‘yancin zub da ciki da aka yi – kuma suna ganin hukuncin koton kolin ya sha ban-ban da abunda jama’a su ke so.