Kuɗaɗen da Ma’akatar Wassani ke Bukata

 

Sunday Dare, ministan wasanni, ya ce ma’aikatar wasanni ta na bukatar miliyan N81 domin cire ciyawa daga filin wasa na MKO Abiola.

A cewar ministan, hukumar kula da muhalli ta Abuje ce ta bukaci ma’aikatar wasanni ta biya kudaden domin a cire musu ciyawar.

Ministan ya ce ma’aikatar wasanni ba ta da adadin kudaden da hukumar kula da muhallin ta nema domin gudanar da aikin.

Ministan matasa da cigaban wasanni, Sunday Dare, ya bayyana cewa zai ɗauki ma’aikatarsu miliyan ₦81 don gyara da cire ciyayin da ba’a buƙata a babban filin wasa na ƙasa ‘MKO Abiola’ da ke Abuja.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a wurin taron ƙarawa juna sani wanda ƙungiyar marubutan wasanni [SWAN] reshen Abuja suka haɗa.

A cewarsa, ma’aikatarsa ta tunkari Hukumar kare Muhallin Abuja (AEPB) don kimanta abin da aikin filin zaici.

Filin, wanda aka gina shi a shekarar 2003, a wuri mai faɗin hekta 29(72 acres) na ƙasa, ya lashe Naira biliyan ₦53.

An raba filin wasan zuwa ɓangarori biyu wato ɓangaren A wanda ke ɗauke da gundarin filin, sai ɓangaren B wanda yake ɗauke da filin ƙwallon kwando, ofishin NFF, filin ƙwallon raga da sauransu.

“Mun tunkari hukumar kula da muhallin Abuja(AEPB) su zo su ga abin da za’a yi don cire ciyayin da sauran muggan ciyayi, sai suka ce mana za su caje mu kuɗi har miliyan ₦81.

“Idan muka gayawa ƴan Najeriya mun yi amfani da miliyan ₦81 wadda bamu da ita, za ka ji hargowar mutane.

“Ba mu da kuɗaɗen, wannan shine dalilin da yasa muke haɗa hannu da masu zuba hannayen jari masu zaman kansu, don farfarɗo da kayayyakin aikinmu,” a cewarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here