Kadarorin da Muka Kwace Daga Gurin Hadimin NSA Monguno – EFCC
Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, a ranar Talata ta bayyana jerin kadarorin da ta kwace daga wani babban hafsan soja a kasar nan.
Kadarorin 24 sun kai darajar N10.9 biliyan, inda ya karu a kan kadarorin N3 biliyan da hukumar ta fara sanarwa a ranar Litinin.
Wani alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Mai shari’a Nkeoye Mana, ya bayar da umarnin kwace kadarorin kuma a mayarwa gwamnatin tarayya a ranar Litinin, kamar yadda Wilson Uwujaren, kakakin EFCC ya sanar.
Amma a wata takarda da Uwujaren ya fitar a ranar Talata, ya bayyana jerin kadarorin 24 da suka kai darajar N10.9 biliyan da aka kwace daga babban hafsan sojan a jihohin Kano, Kaduna, Borno da Cross River.
Kamar yadda hukumar ta bayyana, kadarorin sun hada da gidajen mai 9 masu famfunan siyar da mai 300 duk a jihar Kano, Official EFCC ta wallafa.
Sun hada da wurin siyar da iskar gas mai shaguna 30, dakin taro, rukunin shaguna mai bene hawa uku kunshe da shaguna 28 da gidan bulo duk a Kano.
“Kadarorin 24 duk suna jihohin Kano, Kaduna, Borno da Cross River sun hada da filaye, wurin siyar da iskar gas, gidajen mai masu darajar N10.935 biliyan,” takardar tace.
Hukumar a ranar Litinin ta bayyana cewa, kadarorin ana juya su ne ta hannun hafsan sojan da wasu abokan harkallarsa da suka hada da Marigayi Janar Aminu Maude da wasu kamfanoni da suka hada da Atlasfield Integrated Services Nigeria Limited, Marhaba Events Place, Aflac Plastics da Atlasfield Gas Plant Limited.
Alkali Nkeoye Maha a ranar Litinin ya bayar da umarnin kwace kadarorin sakamakon bukatar da lauyoyin EFCC, Cosmos Ugwu da Musa Isah suka mika.
Read Also:
Alkalin ya bayar da umarnin wallafa sanarwar a jaridu inda ake gayyatar mutane masu ra’ayin bayyana dalilin da zai sa kada a mika kadarorin ga gwamnatin tarayya.
Daga cikin kadarorin akwai:
1. Gidan mai da ke da famfo 16 a Rijiyar Lemo, Kano.
2. Gidan mai da ke kunshe da famfuna 41 mai kallon sakateriyar tarayya a Kano.
3. Gidan mai da ke kunshe da famfuna 39 a titin BUK, Kano.
4. Gidan da ke kunshe da famfuna 31 kan titin Zaria, Kano.
5. Gidan mai da ke kunshe da famfuna 31 kan titin Maiduguri a Kano.
6. Gidan mai da ke kunshe da famfuna 29 a titin Maiduguri, Kano.
7. Gidan mai da ke da famfuna 23 a kan titin Naibawa, Kano.
8. Gidan mai da ke kunshe da famfuna 39 a kan titin Bachirawa, Kano.
9. Gidan mai da ke kunshe da famfuna 51 da ginin bene hawa daya mai Shauna 35 da ke titin Sheikh Jaafar a Dorayi, Kano.
10. Wurin siyar da iskar gas mai Shauna 30 da ke kan titin Zaria a Kano.
11. Marhaba Event Centre da ke titin Guda Abdullahi, Farm Centre, Kano.
12. Rukunin shaguna mai hawa uku da ke kunshe da shaguna 28 kan titin Hadeja kusa da Sheshe Supermarket Kano.
13. Bene mai hawa uku mai kunshe da shaguna hawa 126 kan titin Audu Bako, Kano.
14. Gidan Bulo na Classic da ke kan titin Maiduguri, Kano.
15. Atlasfield Corporate Headquarters da ke lamba L6 kan titin Ahmadu Bello da ke Kaduna.
16. Fuloti da ke Sharada, kusa da gidan mai na A.A. Rano a Kano.
17. Fuloti da ke Yan Rake, kusa da asibitin kashi na Dala, Kano.
18. Fuloti da ke kan titin Kano zuwa Gwarzo, kusa da ofishin Kedco a Kano.
19. Fuloti da ke kan titin Gwarzo zuwa Kano mai kallon masallacin Markaz a Kano.
20. Fuloti da ke titin Sani Marshal, mai kallon Nissan Automobile, Kano.
21. Fili mai girman kadada 11.7 kusa da TINAPA Resort, Adiabo, Calabar.
22. Truck Assembly Plants, Eastern Bypass, Kano.
23. Dakin taro da ke Calabar, Cross River.
24. Aflac Plastics Limited da ke kusa da National Eye Center, Kaduna.