Bayan Yin ƙwacen Waya: Matashi ya Hadu da Ibtila’i

 

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce wani mutum da ake zargi da ƙwacen waya yana cikin mawuyacin hali bayan da mota ta buge shi a lokacin da yake ƙoƙarin tsallaka titi sa’ilin da ya yi yunƙurin tserewa bayan yin ƙwacen waya.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook inda ya ce lamarin ya rutsa da shi ne yayin da yake ƙoƙarin guduwa bayan ya ƙwace wayar wata mata ta hanyar yi mata barazana da makami.

SP Kiyawa ya bayyana cewa sun garzaya da mutumin asibiti inda kuma ya ce ya samu matsalar laka sannan kuma “kansa ya fashe”.

Ƙwacen waya matsala ce da ta yi ƙamari a wasu jihohin Najeriya kuma hukumomin tsaro sun sha bayyana ƙoƙarin da suke na daƙile ta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com