Atiku,Obi Sun Magantu Kan Kisan Nabeehah da Masu Garkuwa Sukai

 

Al’umma a Najeriya, musamman ma a shafukan sada zumunta na nuna ɓacin ransu bayan da masu garkuwa da mutane suka kashe wata budurwa bayan sace ta da ƴan’uwanta a birnin Abuja.

Ƴan bindiga ne suka yi dirar mikiya a gidansu da ke yankin Bwari a Abuja tare da harbe ƴan sanda uku kafin daga bisani su yi garkuwa da ƴan matan da mahaifinsu.

A cewar rahotanni, ƴan bindigar sun halaka Nabeehah – ɗaya daga cikin ƴan matan a ƙarshen mako wadda ɗaliba ce a jami’a bayan da danginta suka gaza biyan kuɗin fansa.

Wani ɗan uwan ƴan matan ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ƴan bindigar sun miƙa wa ƴan uwan Nabeehah gawarta.

Ƴan bindigar dai sun yi barazanar halaka ƴan’uwan Nabeehah da ke hannunsu idan ba a biya su kuɗin fansa ba nan da ranar Laraba.

Biyu daga cikin ƴan sanda uku da ƴan bindigar suka harba a lokacin da suka kai hari suma sun mutu kamar yadda rahotanni ke bayyanawa.

Ƴan sanda sun ce suna yin duk mai yiwuwa domin kuɓutar da ƴan matan sai dai ba su tabbatar da mutuwar Nabeehah ba.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ya ce kisan Nabeehah wata tunatarwa ce cewa ƴan bindiga na cin karensu ba babbaka a ƙasar inda kuma ya yi kira a kawo gyara a harkokin tsaron ƙasar.

Shi ma Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar Labour ya ce batun garkuwa a babban birnin ƙasar manuniya ce kan rashin tsaro a sauran sassan ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com