Cutar Kwalara ta yi Sanadin Mutuwar Mutane 117 a Malawi
Yawan masu kamuwa da cutar kwalara a Malawi ya ninka sau uku a cikin wata biyu, inda hukumomi ke fafutikar yadda za su shawo kan matsalar.
Ya zuwa yanzu, ɓarkewar kwalarar ta yi sanadin mutuwar mutum 117 a ƙasar.
Read Also:
Majalisar dinkin duniya ta ce masu kamuwa da cutar sun karu, daga 1,000 a watan Agusta zuwa 4,200 a wannan wata na Satumba.
A watan Maris ne aka fara samun bullar cutar ta kwalara a kudancin kasar ta Malawi.
Ya zuwa yanzu cutar ta yaɗu zuwa larduna 22 daga cikin 28 na kasar.
Masana sun yi gargaɗin cewar yaɗuwar cutar za ta iya kazancewa a cikin watan Nuwamba, lokacin da damina za ta kankama a ƙasar.
Bayanai daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa ɓarkewar kwalarar ta Malawi ita ce mafi muni a faɗin duniya.