Kwale-Kwale Dauke da ‘Yan Gudun Hijirar Rohingya 150 ya Lalace a Tekun Andaman
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashen da ke kusa da tekun Andama a kudu maso gabashin yankin Asiya, su taimakawa wani kwale-kwale da wuta ta dauke mi shi kusan makwanni biyu kenan, makare da ‘yan gudun hijirar Rohingya 150.
Read Also:
An yi magana mutanen da ke cikin kwale-kwalen ta tarhon tauraron dan adam, inda suka tabbatar da mutuwar wasu daga ‘yan uwansu ciki har da kananan yara.
Sun kuma ce ba su da abinci da ruwan sha. Tun ranar Juma’ar da ta wuce ne, MDD ta yi wannan kira amma har yanzu babu taimakon da ya isa ga mutanen.
Karamin kwale-kwalen kamun kifin ya bar kudancin Bangladesh a makon da ya wuce, a yanzu ya kai sama da kwanaki 21 akan teku. Yawancin wadanda ke cikin kwale-kwalen na kan hanyar zuwa kasar Malaysia ne.
Injin jirgin ne dai ya kasa, kwanaki kadan da fara tafiyar.