Kwale-Kwale ya Nutse da Mutane 20 Yayin da Suke Kokarin Guduwa Daga Harin ‘Yan Bindiga a Jahar Neja
Kwale-Kwale ya kife da wasu yan gudun hijira akalla 20 yayin da suka tsere daga harin yan bindiga a yankin Munya ta jihar Neja.
Mazauna yankin sun bayyana cewa mutanen sun yi wa Jirgin ruwan yawa, sai da ya je tsakiyar ruwa ya kife.
Mutanen da suka kunshi mata da ƙananan yara sun gudo ne daga ƙauyukan Guni da Kurgbaku.
Niger- Aƙalla mutum 20 da suka ƙunshi mata da ƙananan yara ne suka nutse a cikin tafkin Guni-Zumba yayin da suke kokarin guduwa daga harin yan bindiga.
Daily Trust ta tattaro cewa Mutanen da suka nutse ɗin sun baro gidajen su ne lokacin da yan bindiga suka farmaki ƙauyukan Guni da Kurgbaku, ƙaramar hukumar Munya a jihar Neja.
Harin ya faru ne ranar Laraba da safe lokacin da yan bindigan suka mamaye ƙauyukan biyu, bisa tilas mazauna yankunan suka gudu domin tsira da rayuwa.
Read Also:
Wata majiya ta bayyana cewa Mutanen sun nutse ne a kan hanyar tsallake Tafkin zuwa sansanin yan gudun hijira dake Zumba da Gwada a cikin Kwale-Kwale.
hehu Abubakar, wani mazaunin yankin ya shaida wa jaridar cewa kwale-kwalen ya ɗakko mutane fiye da ƙima, kuma hakan ya tilasta masa kifewa a tsakiyar kogin.
Ya ce:
“Yan bindiga sun farmaki yankunan mu da safe, a kokarin guduwa wasu mutane suka kife a kogin Guni-Zumba, saboda nauyin mutane Kwale-Kwalen ya kife a tsakiyar ruwa.”
“A yanzun, ba mu san adadin yawan mutanen da abun ya shafa ba saboda bamu samu nasarar tsamo ko mutum ɗaya ba. Amma zan iya cewa sun zarce 20, mata da yara na ciki.”
Akwai ƙarancin jami’an tsaro
Abubakar ya koka cewa babu isassun jami’an tsaro da zasu kawo musu ɗauki a yankin baki ɗaya.
Wani mazaunin na daban, Michael Madaki, ya ce:
“Yan bindiga sun farmaki ƙauyen Guni a ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja, a kokarin mutane na guduwa Kwale-Kwale ya kife da su a tsakiyar ruwa.”
Kakakin hukumar yan sanda reshen Neja, DSP Wasiu Abiodun, bai daga kiran waya ba kuma bai turo amsar sakonnin da aka tura masa ba kan lamarin.