Cutar Kwalera ta Kashe Mutane 350 a Najeriya

 

Sama da mutum 350 ne cutar kwalera ta kashe a Najeriya a wata tara na farkon wannan shekara, wanda ke nuna ruɓamyar lamarin da kashi 239 idan aka kwatanta da ƙididdigar cutar ta daidai wannan lokacin na bara kamar yadda ƙididdigar hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa, NCDC ta nuna a yau Litinin.

Kwalera wadda cuta ce da ke yaɗuwa ta cikin gurɓataccen ruwan, ba sabuwar cuta ba ce a Najeriya, kuma jami’an kiwon lafiya sun ce tana ta’azzara ne saboda ƙarancin tsabtataccen ruwan sha a ƙasar.

NCDC ta ce mutum 359 sun rasu a tsakanin Janairu zuwa Satumba, amma a daidai wannan lokacin a bara, mutum 106 ne suka rasu.

Haka kuma waɗanda ake tunanin sun kamu da cutar sun hauhawa daga 3,387 a bara, zuwa 10,837 a bana, inda cutar ta fi kama ƙananan yara masu shekara ƙasa da biyar.

Jihar Legas ce kan gaba wajen kamuwa da cutar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here