Kwamishinan ‘Yan Sanda a Raba wa Masu Zanga-Zanga Ruwa da Biskit a Jihar Edo
Kwamishinan ‘yansanda na Edo ya faɗa wa masu zanga-zanga a jihar cewa shi “abokinsu” ne kuma sun je inda suke ne domin su ba su kariya.
Da yake yi wa masu zanga-zangar jawabi a birnin Benin, CP Funsho Adegboye ya ce sun zo wa masu zanga-zangar da ruwa da kuma ɗan abin taɓawa.
Read Also:
“Da ma na sha yin kira a gare ku da mu mazauna jihar Edo mu kafa misali a zanga-zangar lumana, kuma abin da na gani zuwa yanzu sai dai kawai na gode muku,” a cewarsa.
“Ina roƙonku mu cigaba a haka ta yadda sauran jihohi za su yi koyi da mu a zanga-zangar lumana…Za mu ba ku ruwa, da biskit da sauran abin taɓawa.”
Jihar Edo na ɗaya daga cikin jihohin da zanga-zangarsu ba ta yi muni ba a faɗin Najeriya, yayin da ‘yanƙasar ke nuna fushinsu game da tsadar rayuwa da rashin shugabanci nagari.