Kalubalen Dana Fuskanta a Hannun ‘Yan Bindiga – Kwamishinan Labarai na Jahar Neja
Wadanda suka yi garkuwa da kwamishinan labarai na jahar Neja, Alhaji Mohammed Sani Idris, sun sake shi ranar Lahadi da dare.
Sai dai abin al’ajabi shine ko sisi ba a biya ba sai gashi sun sako kwamishinan kamar yadda ya tabbatar.
Bayan sakin shi ne kwamishinan yace da gwamnati ta kuskura ta biya sisi don a sake shi da ya yi murabus bayan fitowarsa.
Minna, Niger – Kwamishinan yada labarai na jahar Neja, Alhaji Muhammed Sani Idris, wanda ya samu ‘yanci daga hannun ‘yan bindiga a daren ranar Alhamis, da ace gwamnati ta biya kudin fansa domin karbarsa, toh babu shakka murabus zai yi.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Idris ya sanar da hakan ne yayin jawabi ga manema labari a Minna, babban birnin jahar inda ya karba bakuncin kakakin majalisar jahar, Rt Honarabul Abdullahi B Wuse da sauran ‘yan majalisar.
Wanne kalubale kwamishinan ya fuskanta a hannun miyagu?
Ya bayyana irin kalubalen da ya fuskanta lokacin da yake hannun masu garkuwa da mutane.
A cewarsa duk da azaba da cutarwar da ya fuskanta a hannunsu, ya jajirce kuma ya dage.
Hakika al’amarin akwai razanarwa.
Da na fita jiya da daddare, na je asibiti don a kara duba jikina kuma komai lafiya lau.
Ni kadai suka sata don sun ganni a babban mutum ne don haka sai da suka dage kwarai don su tabbatar sun samu nasara. Ba cetona aka yi ba kuma ko sisi ban biya ba.
Abin gwanin ban al’ajabi.
Read Also:
Da farko sun fara takura ni suna cutar dani iyakar cutarwa irin wacce ba kowanne d’an Adam ne zai iya jurewa ba; sai dai ubangiji ya taimakeni, saboda na kasance cikin imani.
Na tambayesu idan abinda suke yi daidai ne a wurin Allah, maimakon su rusa ni, sai na fara rusasu.
Bayan nan ne suka fara bani biredi da ruwa. Sun kwance ni sai suka fara amfani da tamfal suna lullubeni idan ana ruwan sama. Sai suka fara nuna damuwa a kaina, ni kuma na cigaba da yi musu wa’azi, sai suka ce in koma wurin iyalina in gansu,” a cewarsa.
Kwamishina ya yabawa gwamnati da bata biya kudin fansa ba
Kwamishinan ya yabawa gwamnan jaharsa akan tsayawa tsayin-daka wurin kin biyan ko sisi ga wadanda suka yi garkuwa dashi, inda yace yana alfahari da jahar Neja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Abin farko da na fara yi bayan sun sakeni shine in tura sakona ga gwamna akan jajircewarsa da kwarin guiwa akan yadda gwamnatin jahar Neja taki amincewa da biyan kudi ga masu garkuwa da mutane kamar yadda hakan ta faru dani.
Sun zo da muryoyi da suka dauka a waya inda nake tabbatar musu da cewa gwamnatin jahar Neja bata biyan masu garkuwa da mutane ko sisi.
Na tabbatar zamu cigaba. Nagode wa gwamnatin jahata akan tsayawa tsayin-daka wurin kare martabarmu.
Lokacin da nake hannun masu garkuwa da mutane duk tunanina yana kan mutanenmu da gwamnatin jahar Neja saboda nasan idan Ubangiji bai kawo dauki ba akwai babbar matsala.
Na gwammaci in rasa raina akan a ciri sisi a biya su. Na fito tsaf ba tare da an biya ko sisi ba kuma babu ko alamar duka a jikina.
Mutane da dama zasu yi mamaki amma kuma ni mai imani ne don haka ba abin mamaki bane. Lokacin da suka saceni na tuna da cewa Ubangiji ya yi alkawarin taimakawa duk wanda yayi imani dashi,” a cewarsa.