Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Imo ya ba da Umarnin Kama Sufetan da ya Mari Direba
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, ya ba da umarnin a kama wani Sufetan ‘yan sanda.
Hakan ya biyo bayan ganinsa da aka yi a cikin wani ɗan gajeren bidiyo yana shararawa wani direba mari.
Tuni dai rundunar ‘yan sandan ta yi ram da jami’in domin ya amsa tambayoyi kan abinda ya aikata.
Owerri, jihar Imo – Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, Muhammed Barde, ya ba da umarnin kama wani Sufetan ‘yan sandan da ya shararawa wani direba mari.
Read Also:
Hakan ya biyo bayan wani ɗan gajeren bidiyo da ya yaɗu a Intanet, da aka hangi ɗan sandan na shararawa wani mai tuƙa mota tafi kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Sufetan ‘yan sandan da ya mari direba ya janyo surutu
Biyo bayan wallafa bidiyon abinda ya faru a kafafen sada zumunta, mutane da dama sun yi tir da abinda ɗan sandan ya yi wa matuƙin motar, inda suka bukaci a hukunta shi.
Kwamshinan ta hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Henry Okoye, ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya ce za a binciko jami’in domin hukunta shi.
Daga baya Okoye ya bayyana cewa an kama jami’in da ake zargi da aikata laifin wanda yanzu haka kuma yake amsa tambayoyi kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.