Adadin Kwanakin da Nake a Jahata – Gwamnan Yobe
Gwamnan Buni yana rike manyan mukamai biyu a jiharsa da birnin tarayya.
Yayinda ofishinsa na gwamna ke jihar Yobe, na shugabancin jam’iyya na Abuja.
Ya bayyana yadda yake raba zaman da yakeyi tsakanin Abuja da Yobe Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwaryan jam’iyyar All Progressives Congress APC, Mai Mala Buni, ya ce yana kwana uku a wata a jiharsa.
A hirar da yayi da BBC, gwamnan yace yana mulkan al’ummarsa kwarai da gaske duk da cewa ba ya zama a jahar.
Read Also:
Buni ya bayyana hakan ne yayin martani kan sukar da ake masa cewa ba ya zama a jihar tun lokacin da ya zama shugaban rikon kwaryan jam’iyyar APC.
Ya kara da cewa aikinsa na shugabancin jam’iyyar ba ya hanashi aiwatar da ayyukansa na gwamna.
“Akan lamarin zama, ba zai yiwu a yi wata daya ban kwashe kwana uku ko hudu a jihar Yobe ba. Kuma ko da na koma Yobe, ba na shela cewa yau zan koma ko gobe zan tafi,” gwamnan yace.
“Zamanin fasaha da muke ciki, ta yaya wani zai ce akwai tarin takardun aiki suna jira na? Ko kafin inzo (hirar) nan, ban san adadin takardun da na duba ba.”