Jami’an kwana-kwana ta Jahar Kano Sun Ceto Dattijo Mai Shekaru 60 Daga Rijiya

 

Jami’in hukumar kwana-kwana ta jahar Kano sun ceto ran wani dattijo mai shekaru 60 mai suna Adamu Manjo.

Wani mutum mai suna Abubakar Shehu Musa ne ya dauki hayan Adamu Manjo don ya yashe masa rijiya amma ya makale a ciki.

Jami’in kwana-kwanan sun turo jami’ansu cikin gaggawa zuwa wurin da abin ya faru a Danshide Quaters suka ceto Adamu Manjo da ransa da lafiya.

Kano – Hukumar kashe gobara ta Jahar Kano ta ceto wani dattijo mai shekaru 60, Adamu Manjo, da ya makale a cikin rijiya a Danshide Quaters a karamar hukumar Dala na jahar, The Punch ta rawaito.

Jami’in hulda da mutane na hukumar, Saminu Abdullahi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa da aka raba wa manema labarai a ranar Litinin a Kano.

The Punch ta rawaito cewa Abdullahi ya yi bayani cikin sanarwar cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin.

Ya ce:

“Wani Zakari Abdulkadir ne ya kira mu misalin karfe 10.02 na safe kuma nan take muka aike da tawagar mu masu aikin ceto kuma sun isa wurin misalin karfe 10.11 na safe.”

Ya ce wani Abubakar Shehu Musa ne ya dauki hayan Manjo ya yashe masa rijiya amma sai ya makale a cikin rijiyar.

Abdullahi ya kara da cewa an ciro leburan daga rijiyar da ransa da lafiyarsa kuma an mika shi hannun wani Alhaji Abubakar Shehu Musa mazaunin Danshide Quarters.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here