Kwankwaso ya Mika Sakon Ta’aziyar Rashin Jagororin Jam’iyyar NNPP
Jam’iyyar NNPP ta na jimamin mutuwar wasu shugabannin jam’iyyar NNPP a hadarin mota.
Jagororin jam’iyyar hamayyar sun gamu da hadarin mota a hanyar su ta komawa Neja daga Abuja.
Rabiu Musa Kwankwaso ya fitar da jawabi ta bakin Hadiminsa, ya na ta’aziyyar rashin da aka yi.
Niger – Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani yayin da ya samu labarin jam’iyyar NNPP ta rasa wasu daga cikin shugabanninta a sakamakon hadarin mota.
A wata sanarwa da Hadimin ‘dan takaran shugaban kasar ya fitar a Facebook, an ji cewa jagororin jam’iyyar NNPP sun rasa ransu da suka yi hadari a hanya.
Kamar yadda Muyiwa Fatosa ya bayyana, hadarin ya auku ne a kan titin Suleja-Lambata a jihar Neja.
Fatosa wanda yake magana da yawun Rabiu Kwankwaso, ya ce wadanda suke cikin motar sun gamu da mummunan rauni, wasunsu suka ce ga garinku nan.
Mutane hudu sun cika
Read Also:
Kamar yadda jawabin da aka fitar ya nuna, wadanda suka riga mu gidan gaskiya su ne shugabannin jam’iyyar NNPP na kananan hukumomin Aagie da Kacha.
Haka zalika akwai shugaban matasa na jam’iyyar NNPP a garin Gbako duk a Neja, da direbansu.
Wasu sun samu rauni
Da yake bayani a shafinsa na Facebook, Ahmed Aliyu Lanle ya ce shugabannin jam’iyyar adawar na kananan hukumomin Gbako, Edati, da Lapai sun samu rauni.
Wadannan mutane su na kan hanyarsu ta komawa gida ne abin ya faru a daidai yankin Old Gawu zuwa Lambata, bayan sun baro garin Abuja a makon nan.
A yanzu wadannan Bayin Allah su na jinya a asibiti, har zuwa lokacin da ake sa ran samun sauki.
Jawabin Kwankwaso
“Na ji bakin cikin samun labarin mutuwar wasu shugabannin reshen kananan hukumomi na jam’iyyarmu ta NNPP a jihar Neja.”
“Bayanan da na samu shi ne mamatan sun rasu ne a wani mummunan hadarin mota a titin Old Gawu, su na hanyar komawa gida.”
-Rabiu Musa Kwankwaso
‘Dan takaran shugaban kasar ya yi addu’ar samun Aljannah ga wadanda suka rasu, tare da rokon Ubangiji ya hana aukuwar irin wannan musiba a nan gaba.