Dalilin da Yasa Kwankwaso bai Samu Shiga Jerin Ministoci 48 ba – Majiyoyi
Shugaban kasa Bola Tinubu ya so nada Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP, a matsayin minista.
An yi wa yunkurin kallo a matsayin wata dabarar Tinubu na samun goyon bayan Kwankwaso da kuma yiwuwar dawo da shi APC.
Sai dai kuma, rashin ganin Kwankwaso a jerin ministocin karshe da aka saki ya ba da mamaki, lamarin da yasa majiyoyi suka yi karin haske a wannan rahoton.
Abuja – Akwai alamu masu karfi da suka nuna cewa Shugaban kasa Bola Tinubu zai nada dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin daya daga cikin ministocinsa.
Tinubu ya yi ganawar sirri da shugaban Kwankwasiyyar sau biyu, wanda daga baya shima ya tabbatar da cewar suna tattaunawa kan yiwuwar yin aiki tare da shugaban kasar.
Read Also:
An tattaro cewa yunkurin na daga cikin kulla-kullan Tinubu na samun goyon bayan tsarin siyasar jigon na NNPP da kuma yiwuwar dawo da shi cikin APC mai mulki.
Sai dai kuma, ga mamakin mutane da dama, Kwankwaso bai samu shiga jerin ministocin 48 da shugaban kasar ya saki ba.
Kwankwaso: Babu ma’ana a karfafa yan adawa Wani rahoto jaridar The Guardian ya ambato majiyoyi na cewa, shugaba Tinubu ya ki amincewa da ra’ayin nada Kwankwaso a cikin majalisarsa ne saboda ya yi imanin cewa babu wata ma’ana karfafa yan adawa, wadanda a karshe za su yi amfani da karfin da suke da shi wajen yakarsu.
Rahoton ya kara da cewa shugaban kasar ya kuma karaya kan yadda sabuwar gwamnatin NNPP ta Kano ta ruguza gine-ginen gwamnati da gwamnatin Ganduje ta gina.
Jigon na APC ya ce:
“Kwankwaso babban bango ne da za a jingina da shi a siyasar Kano. Amma hanya da yanayin yadda tafiyar Kwankwasiya ke tafiyar da kanta yasa goyon bayan da Kwankwaso ke da shi ya dunga raguwa sannu a hankali.
“Hakan kuwa ya faru ne saboda irin gaggarumin hargitsin da kungiyar ke kawowa a siyasar Kano, da kuma karawa Najeriya.”