Dakarun ‘Yan Sanda Sun yi Musayar Wuta da ‘Yan Bindiga a Jihar Katsina

 

‘Yan sanda sun yi musayar wuta da ‘yan bindiga a jihar Katsina, sun samu gagarumin nasara ranar Jumu’a.

Kakakin yan sandan, ASP Aliyu Abubakar ya ce jami’ai sun samu nasarar ceto wani bawan Allah da aka sace a yankin Malumfashi.

Kwamishinan ‘yan sanda, Aliyu Musa, ya yaba wa dakarun ‘yan sandan bisa jajircewar da suka nuna.

Katsina state – Dakarun rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina sun yi artabu da ‘yan bindiga da sanyin safiyar ranar Jumu’a, 25 ga watan Agusta, 2023 kuma sun samu nasara.

Punch ta tattaro cewa yayin musayar wuta da ‘yan ta’addan, jami’an ‘yan sanda sun kubutar da wani dattijo ɗan shekara 65, Hashim Yusuf, wanda aka sace a Hayin Gada, ƙaramar hukumar Malumfashi.

Haka zalika dakarun rundunar ‘yan sandan sun kuma yi nasarar ƙwato shanu 94, Tumaki 17 da kuma babura biyu daga hannun ‘yan bindigan.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu, shi ne ya tabbatar da wannan gagarumar nasara ranar Asabar.

Ya yi bayanin cewa jami’an tsaro sun samu labarin motsin ‘yan bindigan da misalin karfe 2:30 na dare wayewar garin ranar Jumu’a, daga nan suka haɗa tawaga suka tarbe su.

Yadda yan sanda suka yi artabu da yan bindiga Aliyu ya ƙara da cewa yayin da suka yi arangama ne aka yi musayar zuwa mai ban tsoro, wanda daga ƙarshe jami’ai suka ceci mutumin kuma suka kwato kayayyakin.

A kalamansa, kakakin ‘yan sandan ya ce:

“A ranar 25 ga watan Agusta, caji ofis ɗin Kankara suka samu kiran gaggawa game da motsin wasu ‘yan bindiga daga garin Hayin Gada a yankin Malumfashi, inda suka sace Hashim Yusuf, 65.”

“Sun nufi hanyar ƙauyen Lafiya a yankin Kankara, Nan take yan sanda suka tunkari wurin inda suka ci karo da ‘yan ta’adda ɗauke da AK47 da wasu muggan makamai suna ƙoƙarin gudumuwa da mutumin.”

“Yayin musayar wuta, dakarun ‘yan sanda sun nuna jajircewa da gwarzantaka ba tare da gajiya ba har sai da suka tabbatar sun murƙushe barazanar kuma sun ceto mutumin.”

Aliyu ya ce kwamishinan yan sandan Katsina, Aliyu Musa, ya yaba wa jami’an bisa namijin ƙoƙarin da suka yi a bakin aiki, jaridar Within Nigeria ta tattaro.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com