Zan Iya Magance Matsalar Tsaro da Najeriya ke Fuskanta a Halin Yanzu – Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP mai kwandon kayan dadi ya bayyana manufarsa.
Kwankwaso ya bayyana cewa, shi ne zai iya magance matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.
Ya kuma ce, zai kawo karshen matsalolin da ke addabar ma’aikatar ilimi tare da inganta tattalin arziki.
Calabar, Kiros Riba – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Engr Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro da samar da ingantaccen ilimi a kasar idan ya zama shugaban kasa.
Tsohon ministan tsaro kuma gwamnan jihar Kano, ya kuma ce zai bullo da kyawawan manufofin tattalin arziki da za su ciyar da kasa gaba, Leadersip ta ruwaito.
Kwankwaso ya yi wannan alkawarin ne a jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi a cibiyar Kolanut, a wata ganawa da wakilan jam’iyyar NNPP a Calabar.
Ya bayyana cewa zamansa a fadar shugaban kasa, rashin tsaro da ya addabi al’ummar kasar a ‘yan kwanakin nan, zai zama tarihi.
Read Also:
Ya ba da tabbacin samar da ingantaccen ilimi da ingantattun tsare-tsare na tattalin arziki da za su taimaka wajen raya arzikin kasa, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya na gida da na kasashen waje da su hada kai wajen zaben sa a matsayin shugaban kasa.
A kalaman Kwankwaso:
“Zan magance matsalar rashin tsaro, na samar da ilimi mai inganci da ingantattun tsare-tsare na tattalin arziki da za su iya daga al’ummar kasar zuwa kan tudun mun tsira.”
A jawabinsa na farko shugaban NNPP na jihar Kuros Riba, Tony Odey, ya bayyana cewa zaman Kwankwaso a kan kujerar shugaban kasa, matsalar rashin tsaro za ta zama tarihi.
Kwankwaso ne mafita, inji jigon siyasa
Ya kuma bukaci kowa da kowa ya tashi tsaye domin ganin Kwankwaso ya zama shugaban kasa, inji Daily Sun.
A cewarsa:
“Najeriya za ta samu idan aka zabi Kwankwaso. Duk da cewa an mayar da Siyasar Najeriya ta zama wasa da daloli, mun samu wani fitaccen mai gina kasa, wato Engr. Rabiu Kwankwso.
“Kwankwso ya zo da kwarin gwiwar da muka cancanta.
“Najeriya na muradin ganin sauyi kuma mutum daya tilo da zai iya haifar da wannan sauyi shine Kwankwaso.”
“Ya yi yaki da rashin tsaro a lokacin da yake mulki a matsayin gwamnan jihar Kano ba tare da zubar da jini ba. Ina ganin idan muka ba shi dama zai iya yin irin haka a shugabancin Najeriya.”