Kwankwaso ya Magantu Akan Zama Shugaban ƙasa a Zaɓen 2023

 

Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce shi ba wai ya matsa ta dole sai ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da ke tafe.

Jagoran NNPP na ƙasa ya ce shi da makamantansa da suka shiga jam’iyyar, sun yi haka ne domin ceto yan Najeriya.

Ya ce kowane cikakken mai kishin ƙasa ya damu da yanayin tsaro, tattalin arziki kuma yana bukatar samun shugaba nagari.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce shi bai da matsanancin burin dole sai ya zama shugaban kasa a zaɓen 2023.

Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da kafar watsa labarai Channels tv ranar Litinin 30 ga watan Mayu, 2022.

Ya ce shi da kuma masu kyakkyawar zuciya sun shiga New Nigeria Peoples Party wato (NNPP) ne domin canza halin da ake ciki da kuma ceto Najeriya daga rushewa.

Daily Trust ta rahoto Kwankwaso na cewa:

“Abin da yan Najeriya ke cewa shi ne suna bukatar nagari a kowane lokaci, ni zan iya baku tabbacin cewa Ni ba mutum bane da ya matsu dole sai ya zama shugaban ƙasa.”

Mutane sun haji ya kamata a canza – Kwankwaso

Kwankwaso, wanda ke neman ɗare wa kujerar shugaban ƙasa karƙashin NNPP ya kara da cewa mutane sun gaji da tsohon tsari kuma suna bukatar canji.

“Mun gaji da tsohon tsarin da ake amfani da shi yau, shiyasa muka rungumi NNPP domin kawo canji, yadda abubuwa ke wakana a kasar nan yanzu ya yi muni.”

“Kowane mutum ya damu da halin tsaro, tattalin arziki ya raunata, dukan sassan ilimi da al’adu, komai dai ya lalace. Haka ne maƙasudin da ni da makamanta na muka shiga NNPP, muna bukatar haɗuwa wurin ɗaga kudu da arewa”

“Abin da yan Najeriya ke cewa shi ne a 2023, suna son shugaban ƙasa da ya cancanta, mutum mai gaskiya da rikon Amana, wanda zai iya aikin da ake bukata.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here