Rabiu Kwankwaso ya Mayarwa da Gwamna Abdullahi Ganduje Martani

Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana game da tsige Muhammadu Sanusi II.

Tsohon Gwamnan ya fitar da jawabi na musamman ya na yi wa Ganduje raddi.

Kwankwaso ya ce babu abin da ya hada Shugaba Jonathan da cire Sarkin Kano.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya maida martani game da wasu kalamai da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi a kan tsige Sarkin Kano.

Tsohon gwamnan ya fitar da jawabin da ya yi wa take da ‘Ganduje and the blabbering of an imposter’ ta bakin babban sakatarensa, Malam Muhammad Inuwa Ali.

Ya ce: “Hankalin Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ga wani tarin karya da kokarin juya tarihi kuru-kuru da gwamnan Kano da aka kakaba, Abdullahi Ganduje ya fito ya yi.”

Jawabin ya ce: “Abdullahi Ganduje ya yi wannan magana ne wajen kaddamar da littafin daya daga cikin shugabanninmu masu daraja, Goodluck Ebele Jonathan GCFR.”

“A ka’ida bai kamata kowa ya tanka mutum mai neman suna irin Ganduje ba, sai saboda cusa wasu ‘yan Najeriya masu daraja da ya yi, ya na neman ci masu mutunci.”

Muhammad Inuwa Ali a madadin Rabiu Kwankwaso ya fara da taya tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan rubuta littafi game da abin da ya faru da shi a mulki.

Kwankwaso ya ce: “Mun san cewa Ganduje ya na jin kan shi ba kowa ba a duk lokacin da yake tare da Sarkin, mun san cewa ya na da tsohuwar kiyayya da masarauta.”

Tsohon gwamnan ya ce a dalilin haka ne gwamnatin Ganduje ta fara da Sarki Muhammadu Sanusi II, aka nada Sarakunan da za a su iya takawa gwamnatinsa burki ba

Sanata Kwankwaso ya kuma ambaci sukar cin bashin da gwamnatin Ganduje ta ke neman yi a wancan lokaci a matsayin abin da ya sa aka cirewa Sarkin na Kano rawani.

“Wannan shi ya kara sa aka tunbuke Sarki Sanusi II, babu abin da ya hada maganar da Jonathan.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here