Jam’iyyar NNPP ta Baiwa Kwankwaso Tikitin Takarar Shugaban ƙasa a 2023
Jam’iyya mai tashe wato NNPP mai kayan marmari ta damƙa wa Sanata Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa a 2023.
Kwankwaso karkashin sabuwar jam’iyyar zai fafata da sauran yan takara musamman na manyan jam’iyyu PDP da APC.
Shugaban NNPP na ƙasa, Farfesa Rufai Ahmed Alkali, ya ce sun zaɓi Kwankwaso ne bayan dogon nazari.
Read Also:
Abuja – Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ta ƙasa ta ba tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tikitin takarar shugaban ƙasa a babban zaben 2023 da ke tafe.
Jam’iyyar ta ba Kwankwaso tikitin ne ranar Talata bayan tantance shi a babbar Sakatariyar NNPP ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda Aminiya ta rahoto.
Da yake jawabi, shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Farfesa Rufa’i Ahmed Alkali, ya ce sun yi dogon tunani kafin yanke hukuncin tsayar da tsohon gwamnan na Kano a matsayin wanda suke fatan ya gaji Buhari.
Baiwa Kwankwaso tikitin takara a NNPP na nufin cewa tsohon gwamnan zai fafata da yan takara musamman na manyan jam’iyyu PDP da APC a zaɓen 2023.