Gwamnatin Kwara za ta Hukunta duk Wanda ya Kara Kudin Jarrabawar NECO a Jihar
Gwamnatin Jihar Kwara da ke arewacin Najeriya ta ce za ta hukunta duk wani shugaban makarantar da ya karbi kudin da ya wuce naira 22,500 wanda aka amince da shi na jarrabawar kammala sakandire, NECO.
Ma’aikatar ilimi da bunkasa rayuwar jama’a ta jihar ita ce ta yi gargadin a lokacin kaddamar da rijistar jarrabawar ta hukumar jarrabawa ta Najeriya, NECO.
Read Also:
Ainahin kudin jarrabawar naira 17,800 sai kuma wasu tsarabe-tsarabe da ma’aikatar ilimin jihar ta bullo da su wadanda idan aka hada gaba daya kudin ya kai naira 22,500 gaba daya.
Haka kuma gwamnatin jihar ta haramta yi wa dalibai na waje wato wadanda ba ‘yan makarantun ba rijistar jarrabawar ta wannan shekara ta 2022/2023.
A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, Kwamishinar Ilimin jihar Hajia Sa’adatu Modibbo-Kawu wadda ta yi gargadin ta ce matakan da suka dauka na daga cikin sauye-sauyen da suke bullo da su domin magance yadda wasu shugabannin makarantu ke tsawwala wa dalibai kudin jarrabawa a jihar.