Gwamnatin Kwara Zata Soke Biyan Tsofafin Shuwagabanni Fansho

Gwamnatin Jahar Kwara zata dena biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kudin fansho a jahar Kwara.

Wannan matakin ya yi kama da irin wadda gwamnatin Jahar Legas ta dauka a baya bayan nan.

Gwamnan Jahar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a 13 ga watan Nuwamba Gwamnatin Jihar Kwara zata soke dokar biyan tsaffin gwamnoni da mataimakansu kudaden fansho kamar yadda gwamnan jahar ya sanar a shafinsa na Twitter.

Wannan matakin ya yi kama da wadda gwamnatin Jahar Legas ta dauka a baya bayan nan inda ta ce za ta dena biyan tsaffin gwamnonin da mataimakansu kudaden fansho.

Gwamna Abdulrazak yace jahar na bukatar kudade don inganta rayuwar al’ummar jahar, inda ya ce ya yi imanin zai fi dacewa ayi amfani da kudaden jihar wurin magance talauci da samar wa matasa ayyukan yi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here