Dole ne mu Gina Kwarin Gwiwa Mai Karfi Game da Kasarmu – Shugaba Buhari ga ‘Yan Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce akwai wadanda burinsu kawai su ga an wargaza Najeriya.
Buhari ya ce akwai bukatar ‘yan kasar nan su maida hankali tare da samun kwarin gwiwa game da Najeriya.
Saura watanni hudu suka rage shugaban ya sauka, ya ce zai ci gaba da aikin inganta tsaron kasar.
Damaturu, jihar Yobe – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, akwai bukatar ‘yan Najeriya su gina kwarin gwiwa mai karfi game da kasar nan.
Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a fadar sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi a ziyararsa ta jihar Yobe, TheCable ta ruwaito.
A cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina a fitar, Buhari ya ce akwai bukatar ‘yan Najeriya su kauracewa ayyukan da ka iya kawo cikas ga tsaron kasar.
Shugaban ya kuma bayyana cewa, duk da saura masa watanni kadan ya sauka a mulki, amma zai ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da ci gaban tsaron kasar.
A cewar sanarwar:
“Da watanni hudu da nake dashi a matsayin shugaban kasa, zan ci gaba da jajircewa kuma ina fatan yin ritaya a cikin aminci.
Read Also:
“Dole ne mu gina kwarin gwiwa mai karfi game da kasarmu. Ya kamata mu zama ba ma kawo cikas ga lamarin tsaro ta kowacce hanya saboda tsaro da tattalin arziki su ne abubuwa mafi muhimmanci.
“Mun sha wahala sosai yawa a matsayinmu na kasa kuma ina kira gareku da ku kasance masu jajircewa kuma ku tabbatar bamu bari wani ya sake wargaza mu ba.
“Akwai wadanda da gangan ke son ganin sun wargaza Najeriya amma Allah ba zai barsu ba, Allah ya taimaki Najeriya ta farfado.”
Mun kubutar da Yobe daga mamayar ‘yan ta’adda, inji gwamna Buni
Da yake magana a wurin taron, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya shaidawa Buhari cewa, a lokacin da ‘yan ta’adda ke kan ganiyar barna a Yobe, fadar Damaturu sai da ta koma karkashin hannun ‘yan ta’adda.
Sai dai, ya ce a yanzu an samu nasara, domin an fatattaki ‘yan ta’adda, kuma ana ci gaba da samun nasara a kansu, rahoton This Day.
A kalamansa:
“Saidai, a yau abin dubawa ne cewa jihar Yobe na daga cikin jihohin da ka ‘yanta daga mamayar ‘yan ta’addan Boko Haram.”
Duk da yadda aka yaba Buhari, wani jigon siyasa a Najeriya yi masa kudin goro da dukkan ‘yan APC, ya ce kanwar ja ce.