Hukumar Kwastam ta Kama Alburusai 5,200 a Cikin Kayan Amfani

 

Hukumar kwastam ta sake kama wasu alburusai da yawansu ya kai dubu biyar da dari biyu a boye a cikin wasu kayan amfani.

Shugaban ofishin hukumar kwastam da ke Owerri a jahar Imo, Yusuf Lawal, ya koka akan yawaitar safarar makamai zuwa Nigeria.

Ya lissafa wasu manyan kamun makamai da hukumar kwastam ta yi a sassan Nigeria a ‘yan shekarun baya bayan nan .

Hukumar hana fasa kwauri ta kasa wacce aka fi sani da Kwastam ta sanar da kama alburusai da wasu haramtattun kaya da kudinsu ya kama Naira miliyan dari uku da saba’in da takwas da dubu dari bakwai da hamsin da daya da dari tara da talatin da biyar (N378,751,35.00).

Reshen hukumar na Owerri ne ya sanar da cewa ya kama alburusan da sauran kayan a tsakanin watan Nuwamba zuwa Disamba na shekarar 2020, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Yayin da yake sanar da hakan, shugaban ofishin yankin, Kwantirola Yusuf Lawal Psc(+), ya bayyana damuwarsa akan yawaitar safarar makamai.

Ya bayar da misalin yadda aka kama dumbin makamai a Lagos a shekarar 2017, a Kwara a shekarar 2018, da kuma baya bayan nan a Jahar Kebbi.

Ya kara da cewa duk da haka, sai gashi an sake kama wata mota da ke dauke da alburusai 5,200 a ranar 13 ga watan Disamba na shekarar 2020.

A cewar Lawal, an kama motar ne a hanyar Nwezenyi zuwa Ikom ta jahar Kuros Riba bayan samun sahihan bayanan sirri akan yadda aka boye alburusan a cikin sauran wasu kayan amfanin gida.

“Allah ne kadai yasan abinda zai faru da wadannan alburusai sun kai wurin da aka yi niyya, musamman yadda ake fama da matsalar garkuwa da mutane da fashi da makami da matsalar ‘yan bindiga,” a cewarsa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here